Bangaren kasa da kasa: a birnin Trablus fadar mulkin kasar Libya ne za a gudanar da taron share fagen taron ma'aikatun cikin gida na kasashen musulmi da zai tattauna kan kare hakkin kananan yara daga ranar sha uku zuwa sha hudu ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara.