Bangaren kasa da kasa; malamai musulmi da suka halarci taron limamai da malama daga kasashen kungiyar Balkan a ranar alhamis din da ta gabata ashirin da uku ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin hijira shamsiya a cikin wani bayani da suka fitar sun bukaci musulman yankin da su hada kansu da zama tsintsiya guda.