Cibiyar da ke kula harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta gwamnatin hadeddiyar daular larabawa Wam ta watsa rahoton cewa; Thomas de Maziere ministan cikin gida a kasar Jamus a wani zama na manema labarai da ya gudanar a birnin Barlin y ace addinin Musulunci wani bangare ne dab a zai taba rabuwa da al'ummar kasar Jamus ba. Ministan ya fadi haka ne bayan wani zama day a yi da shugabannin cibiyoyi na Musulunci a kasar Jamus inda ya kara da cewa; a yau addinin Musulunci wata hakika ce a tsakanin al'ummar jamus a garuruwa daban-daban na kasar.
581606