IQNA

Kasashe da kungiyoyi da dama na duniya na ci gaba da yin Allah wadai da mummunan harin da haramtacciyar Kasar Isra'ila ta kaiwa ayarin jiragen ruwan

15:49 - June 01, 2010
Lambar Labari: 1932896
Bangaren kasa da kasa: Shugaban Kasar Iran Dr. Mahmud Ahmadi Nejad ya ce harin yana nuni ne da cewa haramtacciyar Kasar ta yahudawan Sahayoniya tana magaganin mutuwa ne.
Bugu da kari Shugaban na Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ya ce Wane abu masu bugun kirji da kare hakkin biladama su ke jira haramtacciyar Kasar ta aikata sannan zuciyarsu ta yi sanyi?
Shi kuwa Sarkin Qatar Sheikh Hamad Ali Tahni ya yi kira da a gaggaunta dauke takunkumin da aka kakabawa Gaza a matsayin girmamawa ga wadanda su ke yi shahada a sanadin harin na haramtacciyar Kasar Isra'ila.
Kungiyar Hizbullah ta Lebanon ta ce harin da yahudawan Sahayoniya su ka kaiwa jiragen ruwan aikin ta'addanci ne wanda ya cancanci duniya ta hukunta ."
Shi kuwa babban magatakardar majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ne da a gudanar da bincike akan harin.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana ranazarta akan mummunan harin da haramtacciyar Kasar Isra'ila ta kaiwa ayarin jiragen ruwa na agaji da su ke akan hanyarsu ta zuwa Gaza.
A gefe daya kasashen Spain da Autria da Masar da Turkiya sun kirayi jakadun haramtacciyar Kasar Isra'ila domin su yi bayani akan harin.


589408
captcha