IQNA

Zaman Taro Kan Harkokin Banki A Mahangar Musulunci A Malazia

20:20 - June 13, 2010
Lambar Labari: 1939071
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da wani zaman taro da zai mayar da hankali kan harkokin banki da cinikayya a tsakanin kasashen musulmi a mahanga ta addinin musulunci a kasar Malazia.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto day a nakalto daga shafin sadarwa na sarawakiic an bayyana cewa, z a fara gudanar da wani zaman taro da zai mayar da hankali kan harkokin banki da cinikayya a tsakanin kasashen musulmi a mahanga ta addinin musulunci a garin Kucink na cikin jahar Sarawak a kasar Malazia. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar wakilai cibiyoyin kudi da harkokin kasuwanci na kasashen musulmi da ma na wasu kasashen dab a na musulmi ba, kuma za a gudanar da taron a kwanaki uku masu zuwa. 595694
captcha