IQNA

Gasar Kur'ani A Yankin Anatoli Na Turkiya

15:03 - June 15, 2010
Lambar Labari: 1940358
Bangaren kasa da kasa : an kawo karshen gasar karatun Kur'ani ta yankin Anatoli da ke tsakiyar kasar Turkiya a ranar ashirin da uku ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a garin Cabkari.



Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga haber 18 ta watsa rahoton cewa; an kawo karshen gasar karatun Kur'ani ta yankin Anatoli da ke tsakiyar kasar Turkiya a ranar ashirin da uku ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a garin Cabkari. Wannan gasar ta shafi ma'aikata da ma'abuta addini da suka hada da malamai masu wa'azi a masallatai da yin khuduba a yankin Anatoli na Turkiya kuma a jiya ne aka kawo karshen wannan gasar a masallacin Sultan Suleiman a garin Cankari kuma wadanda suka shahara da zama na kan gaba a gasar Ankara da Bartn da Bolu sun halarci gurin wannan gasar.

597061
captcha