IQNA

Jami'ar Azhar Ta Maida Martani Kan Limamancin Mace A Britaniya

15:03 - June 15, 2010
Lambar Labari: 1940362
Bangaren kasa da kasa; wani adadi na malamai a jami'ar Azhar sun maida martani kan yadda wata mata ta jagoranci masallata sallar juma'a a cibiyar al'adu ta Musulunci a garin Aksford na kasar Britaniya da cewa wannan limamanci ya sabawa tushen Musulunci.

Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga jaridar kasar saudiya ta Alwatan ta watsa rahoton cewa; wani adadi na malamai a jami'ar Azhar sun maida martani kan yadda wata mata ta jagoranci masallata sallar juma'a a cibiyar al'adu ta Musulunci a garin Aksford na kasar Britaniya da cewa wannan limamanci ya sabawa tushen Musulunci. Muhammad Abu Laila malami a jami'ar Azhar y ace limamancin salla da malama Ahil Rida ta jagoranta ya sabawa tushen addini mace ta jagoranci maza sallar jama'a kuma wannan akwai wata manufa kan hakan.

596991
captcha