IQNA

14:50 - June 17, 2010
Lambar Labari: 1941535

Malazia Za Ta Aike Da Taimako Zuwa Gaza A Cikin Watan Azumi

Bangaren kasa da kasa; Majalisar kungiyoyin da cibiyoyin musulunci a kasar Malazia za ta aike da taimako zuwa ga al'ummar yankin zirin Gaza a cikin watan Ramadana mai zuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da kamafanin dillancin labaran bernama ya bayar ya yi nuni da cewa, majalisar kungiyoyin da cibiyoyin musulunci a kasar Malazia za ta aike da taimako zuwa ga al'ummar yankin zirin Gaza a cikin watan Ramadana mai zuwa. Bayanin ya ci gaba da cewa babban daraktan majalisar Muhammad Azmi Abdulhamid shi ne ya sanar da hakan a jiya, inda ya bayyana cewa za a shigar da wannan taimako ne ta hanyar mashigar Rafah. 598662



captcha