IQNA

An Saka Makabartar Wadi Salam A Cikin Wuraren Tarihin Duniya

14:49 - June 17, 2010
Lambar Labari: 1941538
Bangaren kasa da kasa; Ma'aikatar kula da ala'du ta kasar Iraki ta bayyana cewa hukumar kula da harkokin ilimi da ala'adu ta majalisar dinkin duniya ta saka makabartar Wadi salam a cikin wuraren tarihi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ma'aikatar kula da ala'du ta kasar Iraki ta bayyana cewa hukumar kula da harkokin ilimi da ala'adu ta majalisar dinkin duniya ta saka makabartar Wadi salam dake birnin Najaf mai alfarma a cikin wuraren tarihi na duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa an gina makabartar wadi salam tun sama da shekaru dubu daya da suka gabta, kuma akwai kabrukan annabawa da dama da kuma manayan malamai da bayin Allah daban-daban da aka rufe a wurin tun tsawon tarihi. 598533



captcha