IQNA

Matakin Karshe Na Gasar Kur'ani Ga Sojoji A Saudiya

11:21 - June 19, 2010
Lambar Labari: 1942140
Bangaren kasa da kasa ; an kawo matakin karshe na gasar karatun kur'ani ta musamman ga sojoji a Saudiya kuma daga yau ne ashirin da tara ga watan Khurdad na shekarar hijira shamsiya ne za a fara a garin Riyad fadar mulkin kasar ta Saudiya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Nasij ta watsa rahoton cewa; an kawo matakin karshe na gasar karatun kur'ani ta musamman ga sojoji a Saudiya kuma daga yau ne ashirin da tara ga watan Khurdad na shekarar hijira shamsiya ne za a fara a garin Riyad fadar mulkin kasar ta Saudiya. Mut'ab bin Abdalla bin Abdul aziz mukaddashin rundunat tsaro ta kasar Saudiya da kuma ke kula da harkokin zartarwa ya bayyana cewa; wannan gasar ta shafi duklan bangarori na hardar kur'ani kuma an ware kyautar Riyal na Saudiya dubu dari shida da hamsin ga wadanda suka zao na farko a wannan gasar.

599522
captcha