Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dilalncin labaran iba ya bada rahoton cewa, Wani malamin wahabiyan saudiyya kuma daya daga cikin bayar da fatawa a kasar mai suna Ahmad bin Sa'ad Algamidi ya yi kakkausar suka ga jami'ar Azhar ta kasar Masar, kan amincewar da ta yi a hukumance da mazhabar shi'a a matsayin mazhabar musulunci. Algamidi ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya aike da shi da aka buga a cikin shafin yanar gizo na sabaq, inda ya bayyana cewa bai kamata jami'ar Azhar ta amince da mazhabar shi'a imamiyya a matsayin mazhabar musulunci ba. 599583