Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran maa an bayyana cewa, bangaren farko na daliban jami'ar kur'ani mai tsarki da ke birnin Nablus ya kammala karatunsa tare da gudanar da bikin yaye dalibai na wannan sashe. Bayanin ya ci gaba da cewa adadin daliban na farko da suka fara karatu a wannan reshe su 21 ne suka kammala karatun, kuma jami'ai da dama gami da malaman addinin musulunci sun halartaci taron yaye daliban a Nablus. 599559