Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga tashar sadarwa ta rasid cewa, wasu daga cikin manyan malaman mazhabar shi'a na yankin Kutaif na kasar saudiyya sun yi kira zuwa ga hadin kai tsakanin al'ummar musulmi na duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan kira ya zo a dadidai lokacin da al'ummar musulmi suke fuskantr baraza daga makiya tare da kokarin rarraba kawunnansu domin cimma manufofi na siyasa da danne sauran al'ummomi masu rauni. 599971