IQNA

18:52 - June 21, 2010
Lambar Labari: 1944063

Tunkarar Sahyuniyawa Na Bukatar Hadin Kan Musulmi Da Kirista

Bangaren siyasa da zamantakewa; Daya daga cikin malaman addinin muslunci a Labanan ya bayyana cewa, tunkarar zaluncin yahudawan sahyuniya na bukatar hadin kan musulmi da kirista.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga reshen yada labaransa na birnin Beirut da ke kasar Labanan cewa, Sayyid Ali Makki, mamba a majalisar malaman shi'a a kasar Labanan kuna daya daga cikin malaman addinin muslunci a Labanan ya bayyana cewa, tunkarar zalunci da danniyar yahudawan sahyuniya na bukatar hadin kan musulmi da kirista. Ya ci gaba da cewa a yau an wayi gari hadin kai tsakanin musulmi da kiristoci ya zama wajibi fiye da kowane lokaci, domin fuskantar barazar yahudawan sahyuniya a kan wurarensu masu tsarki.600608



captcha