IQNA

Taron Sabon Tsarin Koyarwa A Kasashen Musulmi A Malazia

18:51 - June 21, 2010
Lambar Labari: 1944065
Bangaren siyasa da zamantakewa; Za a gudanar da wani zaman taro a kasar Malazia na kasa da kasa, wanda zai yi dubi kan irin sabon tsarin koyarwa a kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga bangaren yada labaransa a gabacin nahiyar asia an habarta cewa, za a gudanar da wani zaman taro a kasar Malazia na kasa da kasa, wanda zai yi dubi kan irin sabon tsarin da ya kamata a samar na koyarwa a kasashen musulmi. Zaman taron wanda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da suka hada malaman jami'oi da kuma jami'ai na bangarorin ilimi, zai yi dubi kan hanyoyin koyarwa mafi sauki na zamani da ya kamata a yi amfani da su a kasashen musulmi. 601084




captcha