IQNA

An Amince Da Kudirin Hana Wulakanta Addinai A Kwamitin Tsaro

13:35 - June 22, 2010
Lambar Labari: 1944553
Bangaren kasa da kasa; Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta bada bayanin cewa kwamitin kare Hakkin Bil adama na majalisar dinkin duniya ya amince da kudirin hana wulakanta addinai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar kasa da kasa ta shar alausat an habarta cewa, Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta bada bayanin cewa kwamitin kare Hakkin Bil adama na majalisar dinkin duniya ya amince da kudirin hana wulakanta addinai. Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la'akari da yadda wasu musamman a kasashen turai suke yin amfani da damar fadar albarkacin baki, suke yin tozarci ga addinin Musulunci, hakan ya sanya an amince da wannan kudiri. 601494

captcha