Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren sadarwa da hulda da jama'a na cibiyar yada ilmi da al'adu ta Iran ya habarta cewa, an gudanar da zaman taro kan fikihun Musulunci a birnin Khartum na kasar Sudan, wanda ya samu halartar jami'ai da kuma masana daga sassan kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya samu halartar jakadan Iran a Sudan Turk Abadi, da wasu daga cikin jami'an ofishin jakadancin da kuma wasu malaman kasar. 604133