IQNA

An Fara Gudanar Da Wani Taro Kan Ilmomin Kur'ani A Turkiya

15:30 - June 28, 2010
Lambar Labari: 1947539
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan ilmomin kur'ani a babbar cibiyar bunkasa al'adu da ilimi ta Furat da ke birnin Istanbul na kasar Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar zaman an bayyana cewa an fara gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan ilmomin kur'ani a babbar cibiyar bunkasa al'adu da ilimi ta Furat da ke birnin Istanbul na kasar Turkiya. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taron yana mayar da hanakali ne wajen binciken hanyoyin da za a kara bunkasa ilmomin kur'ani a cikin kasashen musulmi, da kuma sanar da wasu wadanda ba musulmi ba koyarwar kur'ani mai tsarki. 603412



captcha