Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na saffar.org cewa, malamin mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah kuma limamin juma'a a garin Katif na kasar saudiyya sheikh Hassan Saffar ya bayyana cewa, hakkokin dan adam na da matsayin na musamman a cikin fikihun addinin musulunci, wanda dukkanin malamai duk da banbancinsu sun hadu a kan irin wadannan hakkoki. Ya kara da cewa irin wadannan hakkokin za a iya fahimtarsu ma kai tsaye daga ma'anonin ayoyin kur'ani mai tsarki. 605292