IQNA

19:04 - June 30, 2010
Lambar Labari: 1949107

Kafofin Sadarwa Na Shi'a Sun Zama Karfen Kafa Ga Wahabiyanci

Bangaren kasa da kasa; Kafofin yada labarai da sadarwa na mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah sun zama karfen kafa ga akidar wahabiyanci a fadin duniya musamman a kasashen musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kafofin yada labarai da sadarwa na mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah sun zama karfen kafa ga akidar wahabiyanci a fadin duniya musamman a kasashen musulmi. Baynain ya ci gaba da cewa a lokutan baya wahabiya suna cin karensu babu babbaka, sakamakon karancin hanyoyin sadarwa na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah, amma yanzu kasantuwar irin wadannan hanyoyin sun yalwata akan tairaron dan adam da kuma hanyoyin na shafukan yanar gizo, hakan ya kara wayar da kan musulmi da dama kan mazhabar iyalan gidan manzo. 571451


captcha