IQNA

Daliban Kur'ani A Katif Za Su Karbi Takardun Shedar Karatu

15:25 - July 03, 2010
Lambar Labari: 1950100
Bangaren kasa da kasa; Daliban makarantun kur'ani mai tsarki a yankin Katif na kasar Saudiyya za su karbi takardun shedar kammala samun horon haradr kur'ani da kuma karatu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga tashar watsa labarai da rasid an bayyana cewa, daliban makarantun kur'ani mai tsarki a yankin Katif na kasar Saudiyya za su karbi takardun shedar kammala samun horon haradr kur'ani da kuma karatu. Bayanin ya ci gaba da cewa an shirya ma daliban wani kwas ne na bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki da kuma karatu gami da tajwidi a lokacin bazarar bana, inda daga karshe za a gudanar da bikin yaye su tare da basu takardun shedar kammala samun horon. 607721



captcha