Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar kasar Koweiti Alwatan ta watsa rahoton cewa; kasar Italiya da zummar kera kayan abinci na halaliya da suka yi daidai da hukumce-hukumce da koyar shari'ar Musulunci sun nuna kasuwanci na halaliya. An gudanar da hakan ne a birnin Rom fadar mulkin kasar Italiya a ofishin ma'aikatar harkokin waje ta wannan kasar inda mutane da daman gaske suka halarta tare da yin maraba lale da hakan.
607805