Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labarn sananews ya yahabarta a cikin shafinsa na yanar gizo cewa, an shiga bangare na karshe na gasar hardar kur'ani mai tsarki da ta kebanci dalaban makarantun sakandare a kasar Pakistan da ake gudanarwa a birnin Islam-abad fadar mulkin kasar.
Wannan gasar hardar kur'ani dai an saba shirya gudanar da ita a kasar ta kistan, da nufin kara karfafa gwiwar matasa kan harkokin kur'ani, da suka hada da harda da kuma karatun kur'ani.
Yanzu haka dai kimanin dalibai 50 za su shiga bangare na karshe na wannan gasa da a halin yanzu haka take gudana.
608136