IQNA

17:19 - July 04, 2010
Lambar Labari: 1950953

An Kammala Shirye-Shiryen Karbar Masu Ziyarar Hubbaren Imam Kazem (AS)

Bangaren kasa da kasa; A daidai lokacin da ranar shahadar Imam Musa Kazem (AS) ke karatowa 25 ga watan Rajab, masu kula da ayyukan hubbarensa sun bayyana shirinsu na karbar masu ziyara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da kamfanin dillancin labaran brana ya bayar a shafinsa na yanar gizo an bayyana cewa, a daidai lokacin da ranar shahadar Imam Musa Kazem (AS) ke karatowa 25 ga watan Rajab, masu kula da ayyukan hubbarensa sun bayyana shirinsu na karbar masu ziyara da za su zo daga sassa daban-daban na kasar da kuma kasashen duniya.

Daga cikin shirye-shiryen har da daukar kwararn matakan tsaro na bayar da kariya ga masu daga bangaren mahukunta, kamar yadda babban kwamandan rundunar bayar da kariya ga masu ziyara na kasa ya ambata.

Yanzu haka dai an kammala gyara wuraren da masu ziyara ke zuwa a birnin da suka hada cikin hubbaren da kuma sauran wurare masu tsarki.

608408



captcha