Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sheikh Yakub Muzjahi ya bayyana cewa, Allah ya yi wa babban malamin addinin musuluncin nan na kasar Allamah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah rasuwa, a asibitin Bahman da ke kudancin birnin Beirut bayan fama da ciwon anta da ya kai ga kwarar jinni a cikin cikinsa.
Mlalamin wanda shi ne wakilin marigayin a kasar Iran ya bayyana cewa tun 'yan kwanaki da suka gabata ne aka kwantar da Allamah Fadlollah a asibitin Bahman domin kula da lafiyarsa, amma daga ranar Juma'ar da ta gabata ne rashin lafiyar tasa ta tsananta, inda a jiya Allah ya karbi rayuwarsa.
Tun jiya ne manyan mutane da baki daga sassa daban-daban na kasashen musulmi suke ta isa kasar Labanan domin halartar janazar babban malamin wadda za a gudanar a ranar gobe Talata a cikin birnin Beirut idan Allah ya kai mu. Malamai da jami'ai dam asana daga ko'ina cikin duniya suna ci gaba da aikewa da sakonnin ta'aziya.
An haifi Allamah Fadlollah a birnin Najaf Asharaf na kasar Iraki a cikin shekara ta 1935, ya yi karatu a wajen mahaifinsa Sayyid Abdulra'uf Fadlollah, wanda dan asalin kasar Labanan ne amma mazaunin kasar Iraki, daga bisani kuma ya yi karatu a wajen manyan malaman addini na kasar Iraki da suka hada da Ayatollah Uzma Sayyid Khu'i.
Allamah Fadlollah ya fara rubuta littafai na ilmi tun yana kasa da shekaru 20 da haihuwa, a cikin kankanin lokaci ya shahara a tsakanin malamai na birnin Najaf, duk kuwa da karancin shekarunsa a lokacin, saboda basira da Kaifin fahimta da Allah ya ba shi.
A ciki shekara ta 1966 Allamah Fadlollah ya koma kasar Labanan domin ci gaba da ilmantar da jama'a, inda ya kafa makarantarsa ta farko a yankin kudancin birnin Beirut, daga bisani kuma ya ci gaba da bude cibiyoyin ilmi a sassa daban-daban na kasar. Bayan bunkasar makarantar tasa ya bude wasu rassanta a wasu kasashe na yankin gabas ta tsakiya, ya zama malamin da ake komawa zuwa gare shi domin karbar fatawowi na hukunce-hukuncen shari'a, yana daya daga cikin malamai da suke da miliyoyin mabiya a cikin kasashen larabawa da Asia.
609076