Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na yanar gizo dunyabulteni ya habrta cewa, a yau ne musulmin kasar Austria za su gudanar da zaben babban daraktan cibiyar Musulunci ta kasar, wanda za a gudanar a mafi yawan garuruwan kasar da ke musulmi.
Rahoton ya ce wannan zabe yana da matukar muhimmanci ga musulmin kasar, ta yadda za su zabi wanda zai jagoranci harkokinsu musamman ma wadanda suka danganci koyarwar addininsu daidai da yanayin kasar da suke rayuwa.
612396