Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da aka rubuta a shafin yanar gizo na zenebiye an habarta cewa, An sanar da sakamakon gasar da aka gudanar a kasar Turkiya kan haifaffen ka'aba Amirul muminin Ali dan Abu Talib (AS) Wadda ta samu halartar malamai da dalibai da dama daga sassa daban-daban na kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin muhimman abubuwan da gasar ta kunsa har da makaloli, rubutattun wakoki gami da sira. Dukkanin wadanda suka zo a matsayi na farko na biyu ko na uku za su samu kyautuka daidai da matsayin da suka samu a cikin gasar.
612321