Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na kamfanin dillancin labaran Muhit cewa, an fitar da wani rubutaccen tsarin fasahar da Musulunci ya yi amfani da shi a tarihi mai tsawo, wanda marubuta da dama suka ambata a cikin littafan tarihi na zamani. Babbar cibiyar da ke kula da nazari da bincike kan fasahar Musulunci da ked a babban ofishinta a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar, ita ce ta fitar da bayanin.
612317