Salim bin Suleiman Yak mahardacin kur'ani baki daya kuma wakilin kasar Afrika ta kudu a gasar kasa da kasa ta karatun kur'ani mai girma a nan birnin Tehran na jamhuriyar Musulunci tai ran karo na ashirin da bakwai a wata tattaunawa ta musamman da ta hada shi da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa; a Afrika ta Kudu ana samun karuwar masu karatun kur'ani mai girma daga yan shekaru takwas zuwa yan shekaru goma sha takwas a cibiyoyin koyar da karatun kur'ani mai girma da kuma karuwa bude irin wadannan cibiyoyi a kasar.
612560