IQNA

Istighfari a cikin kur'ani/7

Dabi'ar Yan Aljannah A Duniya

17:10 - December 27, 2025
Lambar Labari: 3494411
IQNA – A cikin ayoyin Alkur’ani mai girma, an gabatar da Istighfar (neman gafarar Ubangiji) a matsayin daya daga cikin sharuddan shiga Aljanna kuma dabi’ar ‘yan Aljannah ta duniya.

A cikin suratu Ali-Imrana, an gayyaci mutane zuwa ga gafara da Aljannah mara iyaka (Aya ta 133) kuma bayan ambaton wasu halaye da suka hada da Istighfar, Allah ya ce: “Sakamakon su shi ne gafara daga Ubangijinsu, da gidajen Aljanna, koramu na gudana a cikinsu, kuma suna madawwama a cikinsu, to, albarkar lada ga masu yin aiki”. (Aya ta 136 a cikin suratu Ali Imrana). Wato daya daga cikin sharuddan wadanda suke gaba da sauran mutane a Aljanna shi ne Istighfar.

A cikin ayoyin farko na wannan sura an fara bayanin ladar masu takawa a cikin Aljanna, sannan kuma a cikin bayanin halin da suke ciki na duniya, Allah yana cewa: “ (Su ne wadanda suka yi hakuri, suka fadi gaskiya, wadanda suka sadaukar da rayukansu, kuma suke ciyar da dukiyoyinsu saboda Allah, kuma suna neman gafarar Allah a karshen dare.” (aya ta 17 a cikin suratu Ali Imrana).

A cikin suratu Zariyat, Allah ya yi ishara da kasancewar salihai a cikin gidajen Aljannah da maremari na Aljanna da samun kyautar Ubangiji: “Masu takawa za su zauna a cikin gidãjen Aljanna da maremari, suna karɓar lada daga Ubangijinsu, kuma sun kasance salihai kafin ranar sakamako. (Ayoyi 15-16)

Aya ta 15 ta fara da “karba” kuma ta kare da “Muhsinin (masu kyautatawa)”. Wannan yana nufin samun alheri a cikin Aljanna yana faruwa ne sakamakon kyautatawa a duniya. Sai ya ambaci halaye guda biyu: “Sun yi barci kaɗan a cikin dare kuma suka nemi gafara da sassafe.” (Ayoyi 17-18)

Tsawon kalmomin da ke cikin waɗannan ayoyin suna nuna ci gaba. Wannan ayar tana nuna cewa yin sallah da daddare da neman gafarar alfijir su ne ayyukan mutanen da za su shiga Aljanna. Haka nan yana nuni da cewa da safe, a cikin dukkan masu yin zikiri, neman gafara yana da wani wuri na musamman, kuma ana ganin kololuwar ibada.

 

3495305

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: aljanna sharudda istigfari kyautatawa ibada
captcha