Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa; a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na alhudaacibe an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro kan harkokin banki a mahangar Musulunci a kasar Mauritania wanda zai mayar da hanakali kan hanyoyin bunkasa lamurran kasuwanci tsakanin kasashen musulmi har ma da sauran kasashe da ke bukatar kulla irin wannan dangantaka da su.
Bayanin ya kara da cewa an shirya gudanar da zaman taron ne acikin wata mai kamawa, bisa la'akari da matsalolin harkokin tattalin arziki da ake fama da su a duniya, wanda hakan ya cutar da wasu daga manyan kasashen duniya da tattalin arzikin duniya yake da dangantaka da su kai tsaye.
612727