IQNA

An Bude Azuzuwan Koyar Da Yara Karatun Kur'ani A Turkiya

20:27 - July 13, 2010
Lambar Labari: 1955262
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani shiri na koyar da matasa da kananan yara karatun kur'ani mai tsarki a lokutan hutun bazarar bana a garin Erzurum na kasar Turkiya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na resalehaber ya habarta cewa, an fara gudanar da wani shiri na koyar da matasa da kananan yara karatun kur'ani mai tsarki a lokutan hutun bazarar bana a garin Erzurum na kasar Turkiya, wanda aka fara gudanar tun a cikin makon da ya gabata.

Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar shirin dai ita ce horar da matasa da kananan yara hanyoyin koyon karatun kur'ani mai tsarki tare da kiyaye ka'idojin karatunsa wato ilmin tajwidi.

Malamai da dama daga manyan garuruwan kasar ta Turkiya suna bayar da dukkanin gudunmawa wajen ganin shirin ya kai ga samun nasara, inda suke koyarwa tare da kara kwadaitar da musulmi da su kai yaransu domin su halarci wannan shiri, wanda yanzu haka yake samun halartar daruruwan yara da matasa na birnin.

612656




captcha