Bangaren kasa da kasa; An fitar da wani shiri na bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki a yankin Saihat na kasar saudiyya, wanda za a fara gudanarwa a cikin makon nan tare da halartar matasa na yankin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kur'ani na muzn an habarta cewa, an fitar da wani shiri na bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki a yankin Saihat na kasar saudiyya, wanda za a fara gudanarwa a cikin makon nan tare da halartar matasa na yankin da ma wasu yankuna da suke kusa.
A wannan shiri an kayyade 'yan kasar Saudiyya ne kawai za su iya shiga cikin wadanda za su samu wannan horo, wadanda aka aka riga aka tantance su tun kafin lokutan fara hutun bazarar wannan shekara.
Daga cikin muhimman abubuwan da za a koyar akwai hardar kur'ani mai tsarki wadda ita ce jigon shirin, sai kuma wasu ilmomi na akida fikihu da dai sauransu.
612871