IQNA

Malamin Gwamnatin Labanan Ya Gana Da Sayyid Nasrallah

20:26 - July 13, 2010
Lambar Labari: 1955269
Bangaren siyasa da zamantakewa; Babban malamin gwamnatin kasar Labanan Muhammad Rashid Qabbani ya gana da babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah sayyid Hassan Nasrullah.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na tashar talabijin din almanar da ke birnin Beirut cewa, babban malamin gwamnatin kasar Labanan Muhammad Rashid Qabbani ya gana da babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah sayyid Hassan Nasrullah, inda suka tabo muhimman batutuwa da suka danganci yanayin da ake ciki kasar Labanan da kuma yankin gabas ta tsakiya.

Bayanin ya ce a yayin ganawar bangarorin biyu, Mohammad Rashid Qabbani ya yi ta'aziyya ga sayyid Hassan Nasrullah dangane da rasuwar babban malamin addinin nan na kasar Labanan Ayatollah Allamah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah.

Daga cikin muhimman abubuwan da suka tabo akwai batun kokarin da wasu ke yi na kawo rarrabuwa a tsakanin al'ummar kasar Labanan, inda suka jaddada wajabcin hada karfi da karfe tsakanin dukkain al'ummar kasar domin fuskantar makircin makiya.

612790





captcha