Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da Abbas Ahmad Ali da ya wakilci kasar Tanzania a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa abirnin Tehran ya bayyana cewa, kara yawan lokacin tafsirin kur'ani a cikin gasar da ake gudanarwa yana da babban tasiri wajen fahimtar da masu karatu da ma saurare manonin ayoyin kur'ani da ake karantawa a wuraren gasar da ma sauran wurare.
Abbas Ahmad ya ce daya daga cikin abubuwan da suka kara burge shi a gasar ta birnin Tehran shi yadda aka bayar da muhimmanci ga tafsirin kur'ani maimakon takaituwa da karatu ko harda kawai.
613307