Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran ca.cair na yanar gizo an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan muhimmancin tarbiyantar da yara da kuma matasa musulmi a jahar California, taron da zai samu halartar masana da kuma malaman addini, gami da wakilan cibiyoyin Musulunci na kasar.
Rahoton ya ce babbar manufar gudanar da taron ita ce bayar da dama ga musulmi masu zama a kasashen turai su tarbiyantar 'ya'yansu kan sahihin tafarki na koyarwar addininsu, bisa la'akari da tasirin da bakin al'adu ke yi kan yaro ko matashi.
Musulmin kasar amurka da ma na wasu kasashen turai suna yin iyakacin kokarinsu domin bayar da kyakywan misali wajen tarbiyantar da yaransu kan koyarawar addini, duk kuwa da irin yanayin da suke rayuwa a ciki.
614437