IQNA

An Bude Wani Radiyo Mai Rasulullah (SAW) A Nahiyar Turai

18:31 - July 17, 2010
Lambar Labari: 1957273
Bangaren kasa da kasa; An bude wani gidan radiyo mai suna rasulullah (SAW) a kasar maqdonia da nufin karfafa fahimtar musulmin kasar kan koyarwar addininsu da kuma yin bayani kan manufofin addinin Musulunci ga wadanda ba musulmi ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na egatha.islamyia.net an bayyana cewa, An bude wani gidan radiyo mai suna rasulullah (SAW) a kasar maqdonia da nufin karfafa fahimtar musulmin kasar kan koyarwar addininsu da kuma yin bayani kan manufofin addinin Musulunci ga wadanda ba musulmi ba don su san addinin.

Bayanin ya kara da cewa daga cikin muhimman abubuwan da za a koyar da musulmi har da ilmomi na kyawawan dabi'un Musulunci, koyar da tarbiya da kuma sauran shirye-shirye masu kayatarwa.

615350


captcha