IQNA

Taron Yanki Kan Matsalolin Makarantun Kur'ani A Senegal

16:45 - July 19, 2010
Lambar Labari: 1958686
Bangaren kasa da kasa: taron yanki kan matsalolin da makarantu kur'ani ke fuskanta a kasar Senegal da aka fara a ranar ashirin da shida ga watan Tir na wannan shekara ta dubu daya da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal.


Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ta watsa rahoton cewa: : taron yanki kan matsalolin da makarantu kur'ani ke fuskanta a kasar Senegal da aka fara a ranar ashirin da shida ga watan Tir na wannan shekara ta dubu daya da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal.
A wajen wannan taro an samun halartar malaman addini dam asana daga kasashen Gambiya,Mali,Guinee,tsibirin Komoro,Mauritaniya da kuma mai masabkin baki Senegal. Mahalarta taron za su yi nazari ne kan matsalolin da makarantun kur'ani ke fuskanta domin magancewa da kuma hanyoyi inganta su su zama daidai da tsari irin na zamani da hakan zai bawa masu karatu mada. Kuma irin wannan tsari za a yada shi a fadin kasashen Afrika masu bin tsari karantarwa irin na galgajiya.

616508

captcha