IQNA

An Fara Rijistar Sunayen Masu Shiga Gasar Kur'ani A Ihsa

21:24 - July 29, 2010
Lambar Labari: 1963738
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da rijistar sunayen wadanda suke da sha'awar shiga cikin gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki da za a gudanar a yankin Ihsa na kasar Saudiyya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta rasid ta habarta a shafinta na yanar gizo cewa, yanzu haka an fara gudanar da rijistar sunayen wadanda suke da sha'awar shiga cikin gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki da za a gudanar a yankin Ihsa na kasar Saudiyya a cikin watan Ramadan mai kamawa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasar an saba gudanar da ita a kowace shekara a yankin na Ihsa wanada akasarin mazauna a cikinsa mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah ne.

Babbar cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta yankin ita ce kan dauki nauyin shiryawa da gudanar da gasar, kuma yanzu haka an kamala dukkanin shirye-shiryen ddangane da hakan.

622550













captcha