IQNA

17:29 - July 31, 2010
Lambar Labari: 1964581

Tattaunawa Tare Da Sahyuniyawa Bangaren Na Karfafa Su

Bangaren kasa da kasa; Tattaunawa tare da yahudawan sahyuniya kai tsaye da ake neman tura palastinaw tare da su wani bangare ne karfafa su kan mamaye Qods kuma tamkar amincewa ne da abin da suke aikatawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar alyaum an habarta cewa, daya daga cikin jagororin kungiyar gwagwramaya ta jihadul islami a Palastinu ya bayyana cewa, tattaunawa tare da yahudawan sahyuniya kai tsaye da ake neman tura palastinaw tare da su wani bangare ne karfafa su kan mamaye Qods kuma tamkar amincewa ne da abin da suke aikatawa ta ata'adanci kan al'ummar palastimu.

Ya ci gaba da cewa wasu daga cikin shugabannin kasashen larabawa suna yin matsin lamba kan bangaren palastinawa, sakamakon matsin lamabar da suke fuskanta daga kasashen Amurka da wasu kasashen turai.

623322

captcha