Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro domin tunawa da marigayi Ayatollah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah a birnin London na kasar Birtaniya, wanda cibiyar kua da harkokin addini ta mabiya mazhabar shi'a suka shirya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na SICM na yanar gizo cewa, za a gudanar da wani zaman taro domin tunawa da marigayi Ayatollah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah a birnin London na kasar Birtaniya, wanda cibiyar kua da harkokin addini ta mabiya mazhabar shi'a suka shirya gudanarwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro yana da matukar muhimmanci, domin kuwa zai tabo muhimman abubuwa da suka danganci malamin, da suka hada da rubuce-rubucen da ya yi a bangarori daban-daban na addini.
Ba'ada bayan haka kuma za a duba wasu daga cikin laccocinsa da ya yi kan batutuwa na hadin kai tsakanin al'ummomin duniya, msamman ma musulmi da kirista da kuma tsakanin su kansu musulmin.
625735