IQNA

An Gudanar Da Taro Mai Take Matsayin Kur'ani A Rayuwar Musulmi

17:50 - August 10, 2010
Lambar Labari: 1970915
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani zaman taro mai taken matsayin kur'ani mai tsarki a rayuwar musulmi a birnin Siirt na kasar Turkiya, wanda kwamitin malamai masu bayar da fata na birnin ya shirya gudanarwa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IHA an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro mai taken matsayin kur'ani mai tsarki a rayuwar musulmi a birnin Siirt na kasar Turkiya, wanda kwamitin malamai masu bayar da fata na birnin ya shirya gudanarwa a babban dakin gudanar da taruka na birnin.

Ya ci gaba da cewa taron yana da nasaba ne da ayyana wannan shekara a matsayin shekarar kur'ani mai tsarki a kasar ta Turkiya, inda aka gabatar da jawabai ga mahalarta taron.

Babban mai bayar da fatawa na birnin Siirt sheikh Khalil Chichak ya halarci zaman taron, inda ya gabatar da jawabai, da suka danganci matsayin kur'ani ga rayuwar musulmi.

629790
captcha