Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar arab news ta kasar saudiyya cewa, an sanar da shirye-shiryen masallacin manzon Allah (SAW) da ke birnin Madina mai alfarma wanda malaman da ke jagorancin masallaci suka sanar domin musulmi masu ziyarar masallacin daga sassa na duniyar musulmi.
Masu kula da masallacin mai alfarma sun sanar da shirye-shiryen ne domin bayar da dama ga masu ziyarar su samu masaniya, ta yadda hakan zai taimaka musu a ayyukansu na ziyara.
Rahoton ya ci gaba da cewa fitar bayanin yana da matukar amfani ga masu gudanar da ayyukan umra, wanda dubban musulmi daga kasashen duniya suke gudanarwa.
629498