Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki ta hanyar na'urori a kasar Kuwait da aka shirya domin watan Ramadan mai alfarma, wadda ma'aikatar bunkasa al'adun Musulunci ta kasar ta shirya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar alanba ta habarta cewa, an fara gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki ta hanyar na'urori a kasar Kuwait da aka shirya domin watan Ramadan mai alfarma, wadda ma'aikatar bunkasa al'adun Musulunci ta kasar ta shirya gudanarwa a kasar.
Babban jami'i mai kula da bangaren sadarwa da kuma hulda da jama'a na ma'akatar kula da bunkasa harkokin al'adun Musulunci ta kasar Kuwait ya bayyana cewa, manufar gasarita ce karfafa gwiwar matasa wajen mayar da hankali ga kur'ani mai tsarki.
Ya kara da cewa ta hanyoyin na'ura mai kwakwalwa da kuma shafukan sadarwa na yanar gizo ne ake gudanar da wannan gasa, kuma ta samu karbuwa daga jama'ar kasar.
630409