Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kasar Qatar ya nuni da cewa, Za a gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan matsayin masallacin Qods a wurin al'ummar musulmi a daidai lokacin da ake gudanar da ibadar azumin Ramadan a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka wasu daga cikin kungiyoyin musulmi na kasa da kasa sun sanar da sunayen wakilansu da za su halarci zaman taron, inda za a gabatar da laccoci gami da malkaloli.
Masallacin Qods na da matsayi na musamman a wurin al'ummar musulmi, kasantuwarsa wuri mai tsarki kuma alkiblar musulmi ta farki kafin makka, bayan haka kuma wuri da ke da matsayi a sauran addinai da aka safkar daga sama.
633592