Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto dagashafin sadarwa na Le centre Al Ghadir na yanar gizo an habarta cewa, Cibiyar musulmin kasar Faransa ta Gadir na gudanar da wasu shirye-shirye na musamman da suka ke banci watan Ramadan maia lafarama a yankin Montorvey na kasar ta Faransa.
Rahoton ya ce ana gudanar da shirin ne a kowane bayan kammala sallolin magriba da isha, wato bayan kammala buda baki, inda musulmi kan taru a cikin masallaci domin karatun addu'oi.
Ya kara da cewa sukan gudanar da karatun addu'ar Iftitah da sauran addu'oi da suka kebanci dararen watan Ramadan mai alfarma, tare da halartar malamai da suke amsa tambayoyin addini.
635699