IQNA

Gasar Hardar Kur'ani Mai Tsarki A Masallacin Birnin London

11:34 - August 18, 2010
Lambar Labari: 1976015
Bangaren kasa da kasa; A cikin makon gobe ne za a fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasar Birtaniya a birnin London fadar mulkin kasar, kamar yadda aka saba gudanarwa a shekarun baya a kowane wata na Ramadan.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na iccuk an bayyana cewa, A cikin makon gobe ne za a fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasar Birtaniya a birnin London fadar mulkin kasar, kamar yadda aka saba gudanarwa a shekarun baya a kowane wata na ramadan mai alfarma.

Babbar manufar gudanar da irin wannan gasa dai ita ce karfafa matasa musulmi na kasar Birtaniya wajen mayar da hankali ga karatu da kuma hardar kur'ani mai tsarki, inda matasa da dama daga sassa na kasar kan gudanar da karatu da kuma harda a lokacin gudanar da wannan gasa.

A kan kasa bangarorin da za a gudanar da gasar ne daidai da shekarun masu halartar gasar, harda kan fara ne daga juzu'in farko har zuwa na 25, daga nan kuma a kan bayar da dama ga wadanda suka hardace kur'ni baki daya.

635760




captcha