IQNA

12:12 - August 19, 2010
Lambar Labari: 1976719

Ana Shirin Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Duniya A Aljeria

Bangaren kasa da kasa; Ana shirin fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya a kasar Aljeria, da za ta samu halartar makaranta daga kasashen musulmi daban-daban gami da na larabawa.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na elmojahid an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya a kasar Aljeria, da za ta samu halartar makaranta daga kasashen musulmi daban-daban gami da na larabawa da wasu kasashen nahiyar Afirka.

Gasar dai an saba gudanar da ita a kowace shekara wadda ta kebanci matasa, kuma ana gudanar da karatun kur'ani da kira'a daban-daban amma bisa salon a tartili ba tangimi kamar yadda akan yi a wasu tarukan gasa na kasa da kasa.

Babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasar Aljeria ce tare da hadin gwiwa da ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci suke shiryawa tare da gudanar da wannan gasa a kowace shekara.

636244




captcha