Bangaren kasa da kasa; An wallafa wani tafsirin kur'ani mai tsarki bisa kira'oi goma da suke da tushe a Musulunci daidai da ruwayoyin nassi, wanda wasu daga cikin daliban jami'a da ke karatun addini a jami'ar Gaza suka rubuta.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar Liwa ta kasar Labanan an bayyana cewa, an wallafa wani tafsirin kur'ani mai tsarki bisa kira'oi goma da suke da tushe a Musulunci daidai da ruwayoyin nassi, wanda wasu daga cikin daliban jami'a da ke karatun addini a jami'ar Gaza suka rubuta kuma ake shirin kaddamar da shi.
Rahoton ya kara da cewa dukkanin daliban da suka bayar da gudunmawa wajen rubuta wannan tafsiri dalibai ne masu kara a digiri na biyu a kwas din ilmomin addinin Musulunci a jami'ar palastine da ke garin Gaza.
Yanzu haka dai an kawo kwafi na wannan tafsiri a baje kolin littafan Musulunci da ake gudanarwa a garin Saida da ke yankin palastnu, wanda cibiyar Rawabil Qods ta shirya.
640448