IQNA

16:48 - August 25, 2010
Lambar Labari: 1981407

Za A Kafa Wurin Ajiye Kayayyakin Tarihi Na Kur'ani A Turkiya

Bangaren kasa da kasa; Kwamitin kula da harkokin kur'ani na kasar Turkiya wato masoya kur'ani, zai kafa wani wurin ajiye kayyakin tarihi da suke da dangantaka da kur'ani mai tsarki a kasar.




Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar zaman ta kasar Turkiya cewa, kwamitin kula da harkokin kur'ani na kasar Turkiya wato masoya kur'ani, zai kafa wani wurin ajiye kayyakin tarihi da suke da dangantaka da kur'ani mai tsarki, inda zai ajiye wasu daga cikin abubuwan da ya yi a cikin shekarar nan.

Rahoton ya kara da cewa wannan kwamiti yana gudanar da ayyuka na kur'ani da yake tattarwa a kowace shekara, kuma ya kan gudanar da wasu ayyuka na fasahar rubutun kur'ani da nau'oin rubutu daban-daban.

Kaddamar da wannan wurin ajiye kayayyakin tarihi na kur'ani mai tsarki zai samu halartar wakilan wasu kungiyoyin addini a kasar, da kuma wasu daga cikin baki 'yan kasashen waje.

640238

captcha